'Yan gudun hijira na riguntsminin zuwa Jamus
September 3, 2015An sami wani yanayi mai muni a kasar Hungary lokacin da 'yan gudun hijira suka yi dambe da turereniya dan darewa wani jirgin da suka zaci cewa ya doshi yankin yammacin Turai ne. Tunda sun dade ba su ga jirgin da ya fito yankin ba
Sai dai jirgin na barin tashar da ya dauke su, suka gano cewa 'yan sandan Hungary sun yi musu zamba cikin amince ne, domin sun dakatar da jirgin suka fara kokarin kai su wani sansanin 'yan gudun hijira. 'Yan sandan sun yanke wannan shawarar ne bayan da suka sake bude tashar jirgin Keleti wanda suka kulle na tsawon kwanaki biyu a dalilin 'yan gudun hijirar.
'Yan gudun hijirar dai sun yi ta nuna turjiya, wani mutumi ma janyo wata mata ya yi da danta ya jefa su a kan layin dogon ya kuma ki ya tashi har sai da wasu manyan 'yan sanda suka ciccibesu daga wurin. kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP ya ce da yawa daga cikin 'yan gudn hijiran kin sauka suka yi daga jirgin domin su shiga motocin bus bus din da aka yi musu tanadi domin karasawa da su can sansanonin da aka yi musu tanadi.