1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Wata kungiyar musulmi ta dauki alhakin harin da aka kaiwa New Delhi

October 30, 2005
https://p.dw.com/p/BvNH

Wata kungiya da ba´a san ta ba da ke kiran kanta Inquilab ko kuma juyin juya hali ta yi ikirarin kai harin bama-baman 3 a birnin New Delhi da ya halaka mutane 61. Kungiyar ta yi ikirarin ne a cikin wayar tarho da ta bugawa ´yan jarida a birnin Srinagar hedkwatar bangaren Indiya na yankin Kashmir. Kakakin kungiyar Ahmed Yar Gaznavi ya fadawa kamfanin yada labarun yanki wato Kashmir News service cewa za´a ci-gaba da kai irin wadannan hare hare har sai Indiya ta janye dakarunta daga Kashmir. Wasu tashoshin telebijin sun ce kungiyar wani bangare ne na ´yan takifen kungiyar Lashkar-e-Taiba mai goyon bayan Pakistan. ´Yan sanda sun ce ko da yake ba su da wani bayani game da wanzuwar wannan kungiya, amma suna gudanar da bincike. A kuma halin da ake ciki an tsaurara matakan tsaro a daidai lokacin da ´yan sanda ke ci-gaba da neman wadanda ke da hannu a harin. Tuni dai gwamnatocin kasashen duniya suka yi Allah wadai da harin da cewa wani aiki ne na ta´addanci, kuma ko ba dade ko ba jima za´a cafke wadanda suka aikata wannan danya.