Wata kotu ta yi watsi da zargin cin hanci da ake yiwa Jacob Zuma | Labarai | DW | 20.09.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Wata kotu ta yi watsi da zargin cin hanci da ake yiwa Jacob Zuma

Wani alkali a Afirka Ta Kudu yayi watsi da zargin cin hanci da rashawa da ake yiwa tsohon mataimakin shugaban kasa Jacob Zuma. Hakazalika alkalin yayi fatali da bukatar da lauyoyin dake tuhumar mista Zuma suka gabatar na dage zaman sauraron shari´ar. A bara shugaban ATK Thabo Mbeki ya kori Zuma bisa zargin cin hanci da rashawa, to amma ya ci-gaba da rike mukaminsa na mukaddashin shugaban jam´iyar ANC.