1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Rikice-rikiceGabas ta Tsakiya

Gaza: Ko Masar da EU na da rawar takawa?

Jack Parrock ARH/LMJ
October 22, 2025

Shugaban Masar Abdel Fattah al-Sisi ya nufi Brussels, domin tattaunawa kan yadda kungiyar EU za ta taimaka wajen sake bude mashigar Rafah da kuma bayar da karin taimako zuwa Gaza.

https://p.dw.com/p/52Qvk
Masar | Abdel Fattah al-Sisi | EU | Gaza
Shugaban kasar Masar Abdel Fattah al-SisiHoto: John Macdougall/AP Photo/picture alliance

Tun dai bayan cimma yarjejeniyar kawo karshen yakin Hamas da Isra'ila a yankin Zirin Gaza na Falasdinu, batun shigo da kayan agaji daga Rafa shi ne babban bukatar kasashen da ke fatan ceto rayukan mutane da yunwa ta azabtar cikin shekaru sama da biyu da fara yakin. A yanzu dai hanya daya tilo da agaji ke shiga Gaza ita ce, iyakar Shalom Kerem da Isra'ila ke iko da ita.

Ta ya EU za ta magance matsalar Gaza?

Faransa na kan gaba wajen matsawa EU lamba, kan ta hanzarta farfado da ayyukanta a kan iyaka wanda ta fara a 2005 mai suna EUBAM. "Shirin EUBAM na Rafah na bukatar amincewa daga Masar da kuma hukumomin Isra'ila, domin ci gaba da aiki. A dangane da haka, mu a shirye muke muna bukatar amincewar su duka." In ji babbar jami'ar hulda da kasashen waje ta EU Kaja Kallas.

Gaza: Cimma yarjejeniyar tsagaita wuta

Kungiyar Tarayyar Turai ta fi karkata ga Masar, domin samun gozon bayan cimma wannan aiki. Sai dai kuma Turai ta dade tana sukar matakin Shugaba Al-Sisi kan take hakkin dan Adam, tun bayan abin da suka kira kwace mulki da karfi a 2013. Masar na shirin ci gaba da taka muhimmiyar rawa a Gaza bayan karbar bakwancin taron shugabannin kasashen duniya, inda aka sanya hannu kan yarjejeniyar tsagaita wutar da ta kawo karshen yakin.

Mecece makomar Gaza?

Kuma goyon bayan Masar na iya zama muhimmi ga EU ta samu kujera a teburin kwamitin amintattu na wanzar da zaman lafia da Trump ya kira ‘Board of Peace', wanda ke shirin hada kan kasashen duniya kan makomar Gaza.

A watan Maris na shekarar 2024, EU da Masar sun sa hannu kan wata yarjejeniya mai cike da rudani da ta fi mayar da hankali kan tallafin da gwamnatin Al-Kahira ke bayarwa wajen hana kaura zuwa Tarayyar Turai a kan kudi sama da Euro biliyan bakwai a madadin kudin goro da zai habaka tattalin arzikin Masar din na tsawon shekaru bakwai.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani