1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Rikice-rikiceSudan

Sudan: Yaushe za a daina yaki?

Lateefa Mustapha Ja'afar
June 25, 2026

Ana fargabar sake tabarbarewar al'amura a yakin Sudan, sakamakon yadda mayakan RSF ke shirin kaddamar da gagarumin hari a birnin Al-Obeid da ke da matukar tasiri a kasar.

https://p.dw.com/p/5G4r6
Sudan | Yaki | RSF
Fargabar sake rincabewar yaki a SudanHoto: Rapid Support Forces/AFP

Hukumar Kula da 'Yan Gudun Hijira ta Norway (NRC) ta sanar da hakan ga kamfanin dillancin labaran Jamus dpa, inda ta ce an kange kimanin mutane rabin miliyan na tsawon makonni.

Mutanen na cikin halin tsaka mai wuya na hare-haren jirage marasa matuka daga mayakan na RSF a kowacce rana. Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da Amurka da kasashen Turai da suka hadar da Jamus, sun ce suna ankare da yanayin da ake ciki a yanzu haka a Sudan din.