Uwargidan shugaban Nijeriya Stella Obasanjo ta rasu | Labarai | DW | 23.10.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Uwargidan shugaban Nijeriya Stella Obasanjo ta rasu

Allah yayiwa uwargidan shugaban Nijeriya Olusegun Obasanjo wato Stella Obasanjo rasuwa a yau lahadi bayan an yi mata tiyata a wani asibiti dake kasar Spain. Da a cikin watan gobe Stella Obasanjo zata cika shekaru 60 a duniya. Ba´a ba da karin bayani game da abin da yayi sanadiyar mutuwarta, inji wata sanarwa da fadar shugaban Nijeriya ta bayar. Ita ma ma´aikatar harkokin wajen Spain ta ce uwargidan Obasanjo ta mutu da sanyin safiyar yau lahadi a wani asibiti dake birnin Marbella na kudancin Spain, to sai dai ma´aikatar ta ce ba ta sani ba ko an yi wa Stella din tiyata a asibitin kamar yadda jami´an Nijeriya suka nunar. Ma´aikatar ta ce yanzu haka an aike da gawar zuwa wani ofishin kula da mutuwar ba zato ba tsammani dake Malaga don gudanar da bincike.