Ursula von der Leyen - Zan karawa Birtaniya lokaci | Labarai | DW | 16.07.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ursula von der Leyen - Zan karawa Birtaniya lokaci

Ministar tsaron Kasar Jamus Ursula von der Leyen da ke zama cikin 'yan takarar shugabancin kungiyar tarayyar Turai, ta ce za ta mara wa kudurin karawa Birtaniya wa'adin cimma yarjejeniyar ficewa daga kungiyar EU.

Wannan dai na cikin jerin alkawuran da ministar ta shimfide gaban 'yan majalisun kungiyar tarayyar Turai a wani mataki na nuna alamun sassaucin shugabacin domin samun goyon baya a zaben shugabancin kungiyar. Sai dai ministar tsaron ta Jamaus ta tabbatar da yin murabus daga mukaminta gabannin fara zaben ko za ta yi nasarar zama sabuwar shugabar kungiyar ta EU ko akasin haka.