1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

Ursula von der Leyen za ta sake neman shugabancin EU

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
February 19, 2024

Daga nan ne jam'iyyar CDU za ta gabatar da 'yar takarar mai shekaru 65 da haihuwa a matsayin babbar 'yar takarar jam'iyyu masu ra'ayin rikau na Turai (EPP) a zaben Turai da za a yi a watan Yuni

https://p.dw.com/p/4cYld
Hoto: Markus Fischer/IMAGO

Shugabar hukumar zartarwa ta Kungiyar Tarayyar Turai Ursula von der Leyen za ta halarci taron kwamitin zartarwa na CDU a Berlin a wannan Litinin.

Wakilan jam'iyyar na sa ran von der Leyen ta ayyana aniyarta ta sake tsayawa takara a karo na biyu a shugabancin hukumar ta EU.

Karin bayani:Majalisar EU na shirin bai wa Von der Leyen damar zarcewa

Daga nan ne jam'iyyar CDU za ta gabatar da 'yar takarar mai shekaru 65 da haihuwa a matsayin babbar 'yar takarar jam'iyyu masu ra'ayin rikau na Turai (EPP) a zaben Turai da za a yi a watan Yuni.

Karin bayani:EU: Sake gina Ukraine da kudaden Rasha

Sai dai mambobi za su yanke shawara a taron gamayyar jam'iyyun da ke da ra'ayin rikau EPP a ranakun 6 da 7 ga Maris a Bucharest babban birnin kasar Romaniya. Tsohuwar ministar tsaron Jamus von der Leyen ta kasance shugabar hukumar zartarwar ta EU tun 2019.