1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Turkiyya ta zauna da jakadun wasu kasashe

February 2, 2023

Ma'aikatar harkokin wajen Turkiyya ta kira jakadun kasashen Yamma tara kan dakatar da aiki da suka yi a kasar bisa dalilai na gudun a kai masu hari.

https://p.dw.com/p/4N2da
Türkei Istanbul | Präsident Erdogan bei virtuellem NATO Treffen
Hoto: Presidential Press Office/REUTERS

Jakadun da aka kira sun hada da na Faransa, Burtaniya, Jamus da kuma Holand wadanda suka rufe ma'aikatunsu da ke birnin Santanbul tare kuma da kiran 'yan kasashensu da su yi takatsantsan game da barazanar huce haushi da suka iya fuskanta biyon bayan kona Alkur'ani mai girma da aka yi a wasu kasashen Arewacin Turai yayin wata zanga-zanga.

To sai dai ministan harkokin wajen Turkiyya Süleyman Soylu ya zargin kasashen da neman tunzura jama'a tare kuma da neman raunana wasu harkokin cikin gida na Turkiyyar musanman fanni yawon buda ido, yayin da shi kuma kakakin gwamnatin Turkiyar ya kira matakin kasashen da abin da bai dace ba. 

A karshen watan Janairu ne dai a wasu birane na kasar Sweden da Danemark wasu masu zanga-zanga su ka kona Alkur'ani mai girma domin nuna fushinsu kan kin sahalewa kasar Sweden shiga kungiyar kawancen tsaro ta NATO da Turkiyya ta yi a matsayinta na mai karfin fada a ji a kungiyar.