1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tony Blair na ci-gaba da ganawa da shugabannin Gabas Ta Tsakiya

July 24, 2007
https://p.dw.com/p/BuFc
A karon farko tun bayan karban sabon aikinsa na wakili na musamma a yankin GTT a yau tsohon FM Birtaniya Tony Blair ya gana da shugaban Falasdinawa Mahmud Abbas a birnin Ramallah na Gabar Yamma da Kogin Jordan. Abbas ya nunar da batutuwan da suka tattauna a kai sun hada da irin goyon bayan da bangarorin nan hudu da ke shawarta batun samar da zaman lafiya GTT zasu bawa hukumomin Falasdinu. Da farko Blair ya gana da shugaban Isra´ila Shimon Peres a Birnin Kudus. ´Yan siyasan biyu sun ce akwai kyakkyawar damar maido da shirin zaman lafiyar GTT bisa turba. In an jima Blair zai koma Birnin Kudus inda zasu ci abincin dare da FM Isra´ila Ehud Olmert wanda yayi alkawarin daukan matakan karfafa shugaba Abbas akan kungiyar Hamas wadda ke iko da Zirin Gaza.