Taron magance rikicin Libiya | BATUTUWA | DW | 19.01.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

BATUTUWA

Taron magance rikicin Libiya

Bangarorin da ba sa ga majici da juna da masu taimaka musu a rikicin kasar Libiya na halartar taron neman hanyoyin magance rigingimun a Berlin na kasar Jamus a wannan Lahadi.

Bisa gayyatar gwamnatin kasar Jamus, a wannan Lahadi ake gudanar da wani taro a birnin Berlin na Jamus tsakanin masu rikici da juna a kasar Libiya da kasashen ketare da ke tallafa musu. Ita ma Majalisar Dinkin Duniya za ta halarci taro da zai gudana a fadar shugabar gwamnatin Jamus da ke fata taron zai bude hanyar samar da zaman lafiya a gaba dayan yankin arewacin Afirka.

Babban burin gamnatin tarayyar Jamus shi ne tabbatuwar 'yancin kan kasar Libiya da shirin sulhu na cikin gida a Libiya, kamar yadda takardar gayyatar taron ta nunar. Sai dai kasar na nesa da wannan, saboda yakin da ake yi tsakanin gwamnatin birnin Tripoli da duniya ta amince da ita karkashin Faeez al-Sarraj da madugun 'yan tawaye Janar Khalifa Haftar da ke iko da mafi akasarin yankunan kasar da rijiyoyin mai masu yawa. Halin da ake ya kara dagulewa saboda shiga cikin rikicin da wasu manyan kasashen duniya suka yi. Ga misali Turkiyya tana goyon bayan gwamnatin Tripoli, yayin da Rasha da Masar da Daudiyya da Hadaddiyar Daular Larabawa ke marawa Haftar baya. Ita kan kungiyar Tarayyar Turai kanta ya rabu saboda rikicin inda ake jita-jitar cewa Faransa na goyon bayan Haftar, ita kuma Italiya da ta yi wa Libiya mulkin mallaka na tallafa wa Sarraj.

Baya ga manyan masu rikici a Libiya, gwamnatin Jamus ta kuma gayyaci shugabannin kasashe da ke da hannu kai tsaye cikin rikici da wakilai na kungiyar EU da na tarayyar Afirka da na kungiyar kasashen Larabawa sai kuma babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres. Sai dai kasar Tunisiya da ke makwabtaka da Libiya ta yi mamakin rashin ba ta goron gayyata domin a cewarta ta fi kowace kasa jin radadin rikicin na Libiya. Sai dai mai matgana da yawun gwamnatin Jamus Ulrike Demmer ta ce wannan ba shi ne matakin karshe ba.

Ko Jamus za ta yi nasara a matakin da ta dauka na yin sulhu tsakanin masu rikicin na Libiya. Tim Eaton masanin yankin arewacin Afirka ne a cibiyar nazarin harkokin siyasar duniya ta Chatham House da ke birnin London ya nuna shakkunsa.

Duk da haka dai a ranar Alhamis ministan harkokin wajen Jamus Heiko Maas ya yi nasara muhimmiya a batun da kawo yanzu ya cije, inda Haftar ya tabbatar masa da shirinsa na tsagaita bude wuta bayan ganawar da suka yi a birnin Bengazi da ke zama tungar Haftar.

Sauti da bidiyo akan labarin