1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

EU ta fara cire Birtaniya a dangi

Suleiman Babayo / LMJJune 29, 2016

Shugabannin kungiyar kasashen Tarayyar Turai sun yi taro a karo na farko ba tare da Birtaniya ba, bayan zaben raba gardama da 'yan kasar suka nemi fita daga cikin kungiyar.

https://p.dw.com/p/1JFvC
Taron EU na farko ba tare da Birtaniya ba
Taron EU na farko ba tare da Birtaniya baHoto: Reuters/E. Vidal

Sai dai shugabannin kungiyar ta EU, sun jaddada matsaya bisa cewa muddin Birtaniya tana bukatar ci gaba da kasance cikin kasuwancin bai daya da sauran kasashen, tilas ta amince da tsarin shige da fice na bai daya. A yayin taron da suka gudanar a birnin Brussels na kasar Beljiyam da ke zama shelkwatar kungiyar, sun tabbatar da cewa babu yadda za a yi Birtaniya ta samu wani gata da kasuwanci tare da sauran mambobin kasashen 27 bayan ta fita, ba tare da ta amince da tsarin zirga-zirgar mutane na bai daya ba.

Shugaban majalisar Tarayyar Turai Donald Tusk da na hukumar Tarayyar Turan Jean-Claude Juncker
Shugaban majalisar Tarayyar Turai Donald Tusk da na hukumar Tarayyar Turan Jean-Claude JunckerHoto: Reuters/F. Lenoir

Donald Tusk shi ne shugaban majalisar gudanarwar kungiyar ta EU ya kuma yi karin haske bayan taron na wannan Laraba:

Mutane da dama ba sa farin ciki

"Mun kuma tattauna bisa cewa akwai mutane da dama a kasashen Turai da ba sa farin ciki da halin da ake ciki wadanda suke bukatar ganin mun yi abu mai kyau. Idan za a tuna an kwashe fiye da shekaru 10 Turai tana cike da fata, wajen da ya kamata mu koma ke nan."

Tusk ya kara da cewa wannan ke zama taron farko na kasashen 27 bayan ficewar Birtaniya, domin haka ya yi wuri a yanke wani hukunci. Kuma shi ya sa aka fara da duba makomar siyasa a kasashen 27 wadanda za su sake taro ranar 16 ga watan Satumba mai zuwa a birnin Bratislava. Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta ce babban abin da yanzu kasashen suka saka a gaba shi ne tabbatar da samun bunkasa na tattalin arziki:

"Duk wani tsinkaye a kan tattalin arzikinmu a wannan lokaci ya nuna babu karin bunkasa. Domin haka za mu mayar da hankali bisa ci-gaba mai dorewa da bunkasa kan rashin da muka samu sakamakon ficewar Birtaniya daga cikin mu."

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel
Shugabar gwamnatin Jamus Angela MerkelHoto: picture-alliance/dpa/S. Lecocq

Bacin ran shugabannin EU

Shugabar gwamnatin ta Jamus Merkel ta nuna takaicin fitar Birtaniya daga kungiyar Tarayyar Turai, amma ta girmama zaben da mutane suka yi, kuma ta ce Birtaniya za ta ci gaba da samun duk wana gata a matsayin mamba, har zuwa lokacin da za ta bar kungiyar baki daya. Shugaban hukumar Tarayyar Turai Jean-Claude Jucker ya amince da shirin sauye-sauye amma ya ce bisa aiwatar da manufofin kungiyar. Masu zabe a Birtaniya sun amince da fita daga kungiyar ta Tarayyar Turai wato EU musamman saboda batun katse yawan bakin masu kaura zuwa kasar. Sai dai yanzu zai yi wuya su samu abin da suke bukata muddin za su ci gaba da hulda ta kut-da-kut da sauran kasashen na kungiyar Tarayyar Turai.