1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taro tsakanin jami'an gwamnati da musulmin Jamus

YAHAYA AHMEDSeptember 26, 2006

Gwamnatin tarayyar Jamus ta kira wani babban taro, inda jami'anta za su tattauna da wakilan addinin islama a nan Jamus, kan batun inganta halin zaman cuɗe ni in cuɗe ka da sauran al'aumman ƙasar, wato Jamusawa da kuma waɗanda ba musulmi ba.

https://p.dw.com/p/BvTI
Ministan harkokin cikin gidan Jamus, Wolfgang Schäuble.
Ministan harkokin cikin gidan Jamus, Wolfgang Schäuble.Hoto: AP

Tuni dai, kafin a fara taron ma, ƙungiyoyin islama da dama sun fara sukar manufar da hukumomin Jamus suka saynya a gaba, ta shirya shi. Ƙungiyar nan ta Turkawa Milli Görüs, wadda ta fi sauran ƙungiyoyin islaman yawan mambobi a nan Jamus ta yi suka ga son zuci da aka bi wajen zaɓan waɗanda za su halarci taron. Yawan ’yan ƙungiyar dai ya fi dubu 30. Amma duk da haka ba a gayyace ta ta tura wakilai zuwa taron ba, wanda kuma aka ce na tattaunawa ne tsakanin wakilan musulmi da na gwamnati. A halin yanzu ma dai, jami’an leƙen asirin Jamus na sa ido ne kan ƙungiyar, wai saboda tuhumar da ake yi mata, na samun masu tsatsaurar ra’ayin islama a cikin mambobinta. Janar Sakatare na ƙungiyar, Oguz Ücüncü, ya soki lamirin shirin ne ma gaba ɗaya, da bayyana cewa:-

„Abin da muke yi wa suka game da shirin shi ne, rashin buri da kuma alƙiblar da za a mai da hankali a kansu a lokacin taron. Sabili da haka ne ma hukumomin da ke shirya taron har ila yau ke ɗari-ɗari wajen bayyana jerin sunayen waɗanda aka gayyata, a ɓangaren musulmin. Wato kamar dai wani shirinsu ne da suka tsara, wanda suke kira da sunan taro da al’umman musulmin Jamus.“

Duk da cewa dai ba a gayyaci ƙungiyar ta Milli Gürüs bisa manufa ta halarci taron ba, za ta iya samun wakilci ƙarƙashin laimar uwa uban ƙungiyoyin islama na Jamus, wato Majalisar Ƙoli ta Musulmin Jamus, wadda take da jami’ai a cikinta.

Sauran ƙungiyoyin islaman da hukuma ta amince da su, waɗanda kuma za su tura wakilai zuwa gun taron, sun haɗa ne da Gamayyar Islama ta gwamnatin Turkiyya a nan Jamus, da Ƙungiyar al’adu ta islama da kuma ƙungiyar ’yan Alevit na Jamus.

Su dai ƙungiyoyin islaman na fargabar cewa, irin mutanen da aka gayyato zuwa taron, ba su ne za su iya wakilcin duk musulmin Jamus ba. Da yawa daga cikinsu dai, ba su da jiɓinta da addinin sosai ko kuma da ƙungiyoyin islaman. Alhali kuwa, su ƙungiyoyin ne sahihan wakilan musulmi a nan Jamus. Oguz Öcüncü, ya ba da misali a nan, da yin la’akari da cocin Katolika:-

„Bai kamata dai shirin ya bambanta da na wasu addinai ba. Idan alal misali za a takalo batun da ya shafi ɗariƙar Katolika, ba duk wani ɗan ɗariƙar ne ake gayyata hakan nan ba. Ana damawa ne da masu jan akalar cocin katolikan. Haka kuma ya kamata a yi da musulmi. Ƙungiyoyin da ke wakilcinsu ne ya kamata a dama da su, a tattauna da su, waɗanda kuma suka san abin da suke ciki, amma ba da kowa da za a iya samu a kann titi da yake kiran kansa musulmi ba.“

Shi dai ministan harkokin cikin gida na tarayya da ma’aikatansa, ba su yi la’akari da wannan batun ba, kafin su zaɓi waɗanda suke son ganinsu a taron. Ma’aikatar harkokin cikin gidan dai ta shafe fiye da wata shida tana tuntuɓar musulmi, ana kuma binckensu, kafin ta tsara jerin sunayen waɗanda za ta gayyata. A halin yanzu dai akwai sunayen waɗanda ƙungiyoyin islaman ba su amince da su ba, a jerin waɗanda hukuma ta gayyaci su halarci taron kamarsu Necla Kelek, baturkiyan da ta yi tashe wajen sukar lamirin islama, ko kuma lauyan nan ta Berlin mai fafutukar wai kare hakkin mata musulmi, Seyran Ates. Ibrahim El-Zayat, wani babban jami’in Majalisar Ƙoli ta musulmin Jamus, ya yi suka ga wannan salon da hukuma ke bi da cewa:-

„Idan a wata ƙasar musulmi ne ministan harkokin cikin gidan ƙasar ya kira wani taron kan addinin kirista, ya gayyaci waɗanda ke kiran kansu kiristoci a baka kawai, amma waɗanda ba su da wani abin da suka sanya a gaba, sai sukar lamirin addinin kiristan, kamarsu Eugen Drewermann da Hans Küng ko kuma Karl-Heinz Deschner a nan Jamus, ai da sai in ce irin kururuwar da za a dinga yi zai fi na waɗanda musulmi ke yi yanzu.“