Takun saka a taron G20 | Labarai | DW | 28.06.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Takun saka a taron G20

Ganawa tsakanin shugaban Amirka da na China gami da kasuwanci tsakanin kasashen ya dauki hankalin taron G20 da ke gudana a Japan.


Batun harkokin kasuwanci na ci gaba da samun tagomashi a taron manyan kasashe da ke sahun gaba wajen karfin tattalin arziki a duniya na G20 da ke gudana a kasar Japan. Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel tana fata za a samun mafita kan kiki-kaka tsakanin kasashen Amirka da China wadanda suke gaban gaba wajen karfin tattalin arziki a duniya. Yayin da ake shirin ganawa tsakanin Shugaba Donald Trump na Amirka da takwaransa Xi Jinping na China a gefen taron.

Haka kungiyar kasashen Tarayyar Turai suna tattauna samun kasuwanci ba shinge da kasashen kudancin Amirka. Ana samun dari-dari a kasuwar hannun jari a duniya saboda rashin tabbas na abubuwa da za a cimma a wannan taro na G20 da ke gudana a kasar Japan.