1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ayar tambaya kan makomar sojin Jamus a Mali

Peter Hille MAB
January 31, 2022

Shekaru tara bayan jibge sojojinta a Mali, Jamus na nuna damuwa game da jinkirin shirya zabe a kasar, yayin da fadar mulki ta birnin Bamako ke nesanta kanta daga kasashen Yamma tare da fara neman sabbin abokan hulda.

https://p.dw.com/p/46Jfl
Mali Bundewehr UN-Einsatz
Yara na sha'awar yadda sojojin Jamus ke gudanar da aikinsu a MaliHoto: Alexander Koerner/Getty Images

kusan sojojin Bundeswehr 1,300 ne ke jibge a Mali, wanda ke zama aikin sojin Jamus mafi girma a ketare. Ana ci gaba da kai musu kayayyaki aiki a sansanin da aka tsugunar da su. Ko da a makon da ya gabata, sai da sojojin Jamus suka karbi wata motar sulke a filin jirgin saman Bamako. Sai dai ba a san tsawon lokacin da rundunar ta Bundeswehr za ta ci gaba da aikawa da kayan aiki da sojoji zuwa kasar da ke yammacin Afirka ba.

A karshen watan Mayu ne wa'adin sojojin Bundeswehr zai kare na shirin horarwa na EU EUTM da na wanzar da zaman lafiya na MDD (MINUSMA). Kuma babu tabbas cewa majalisar dokokin Jamus ta Bundestag za ta tsawaita wannan aikin. A Berlin, ana nuna bacin rai game da gwamnatin Assimi Goïta, wanda ya kwace mulki a watan Mayun 2021 kuma ya nada kansa shugaban rikon kwaryar Mali.Agnieszka Brugger, kwararriya kan harkokin tsaro na jam'iyya mai mulki ta Greens, ta yi tsokaci kan dage zaben na Mali, in da ta ce  "Komawa kan kundin tsarin mulkin kasar wani muhimmin sharadi ne na cudanya tsakanin kasashen duniya da Mali. Ko shakka babu hukunce-hukuncen na gwamnatin rikon kwarya, sun haifar da bacin rai, sakamakon yadda aka takura 'yancin zirga-zirga na sojojin kasa da kasa da suka hada da sojojin Jamus, misali ta hanyar hana shawagin jirgin sama."

Magazin Global 3000 | 20.09.2021
Tsaro bai inganta ba shekaru tara bayan jibge sojin Jamus a MaliHoto: WDR

Alamun farko na tsamin dangantaka tsakanin Mali da Turai

A karon farko, gwamnatin Mali ta ki amincewa da wani jirgin sojin Jamus da ke dauke da sojoji 75 ya yi shawagi a sararrin samaniyarta. Sannan, Bamako ta bukaci sojojin Denmak da ke aikin karkashin rundunar "Takuba" ta Turai da su fice daga cikin gaggawa saboda rashin amincewar Mali. Wannan dai alama ce ta kara nisanta kanta daga kawayenta na Turai, musamman daga tsohuwar uwargijiyarta ta Faransa. Sai dai Florian Hahn, kakakin kwamitin tsaro na bangaren 'yan adawa a majalisar dokokin Jamus ta Bundestag ya ce ko shakka babu, yana da amfani ga kasar Mali ta ci gaba ta zama kasa mai bin tsarin mulkin dimokuradiyya.

Ya ce "Babu wata tantama game da wannan batu. Amma kuma dole ne mu gane cewa gwamnatocin da suka gabata da aka zaba ta hanyar dimokuradiyya ba su samu karbuwa a tsakanin al'ummar kasar, kamar yaddda gwamnati mai ci a yanzu ta samu ba. Abu mai muhimmanci shi ne a samu daidaituwar lamaru. Abu ne mai muhimmanci jama'a su kasance cikin farin ciki kuma dole ne mu goyi bayan haka. Idan muna koma ga goyon bayan kasashen da ke kan tsarin dimokuradiyya ne kawai, to zan iya cewa: Ba sa bukatar mu...."

Mali I Russland I Militär
Sojin Mali na alfahari da dasa tutar Rasha a kusa da ta kasarsuHoto: Nicolas Remene/Le Pictorium/imago images

Dakarun "Wagner" na neman maye gurnin sojin Turai

Bayanan da sojojin Amirka suka fitar sun yi nuni da cewa daruruwan haya na Rasha na kungiyar "Wagner" sun riga sun fara aiki a kasar Mali. Samun karin karfi a yankin Sahel zai sa Rasha ta iya fadada tasirinta a Afirka - kuma a lokaci guda ta sami madogara wajen tataunawa da kasashen yamma a kan rikicin Ukraine. Bugu da kari, Moscow na iya yin sha'awar albarkatun ma'adinai irin su bauxite, zinariya da lu'u-lu'u da ke yankin. Dama yawancin 'yan kasar Mali na zargin kasashen Turai da wawushe arzikin karkashin kasa da Allah ya hore musu.

Ko da dan siyasar Jamus Florian Hahn, sai da ya ce lokacin da sojojin kasashen yamma za su fice daga Mali,  Rasha ce za ta maye gurbinsu. Ya ce "Rashawa sun riga sun shiga nahiyar Afirka karkashin kungiyar da ake kira Wagner Group, mun san haka daga rahotannin da muke samu. Sanin kowa ne cewa Rasha ba ta aiki da sunan Turai, amma don amfanin kanta kawai."