SPD za ta bayyana matsayinta | Labarai | DW | 03.03.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

SPD za ta bayyana matsayinta

Jami'yyar SPD ta Jamus ta ce ba ta da wani shakku a game da kada kuri'ar amincewa da kafa gwamnatin hadaka tare da jam'iyyar shugabar gwamnti Angela Merkel wato CDU.

A gobe Lahadi aka shirya magoya baya jam'iyyar kusan dubu 463 za su ka'da kuri'a a game da batun shiga cikin gwamnatin hadakar. Kuma idan har jami'yyar ta SPD  ta ka'da kuri'ar amincewa da gwamnatin to hakan zai bai wa Jamus din damar ficewa daga cikin wani tarnakin siyasar da ta samu kan ta a cikin watanni biyar bayan zaben 'yan majalisun dokoki.