1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Spain na son ba da gudunmawar tsaro a Falasdinu da Ukraine

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
January 8, 2026

Spain na cikin masu sukar lamirin Isra'ila kan yakin Gaza, har ma ta amince da Falasdinu a matsayin 'yantacciyar kasa.

https://p.dw.com/p/56WAF
Firaministan Spain Pedro Sánchez ke gaisawa da shugaban Amurka Donald Trump
Firaministan Spain Pedro Sánchez ke gaisawa da shugaban Amurka Donald TrumpHoto: Evan Vucci/AFP

Firaministan Spain Pedro Sanchez ya ce a shirye kasarsa ta ke, ta aike da dakarun tsaronta Falasdinu, domin aikin tabbatar da tsaro da wanzuwar zaman lafiya a yankin, mai fama da rikici tsawon shekaru.

Mr Sanchez ya shaida cewa matukar aka bai wa kasarsa wannan dama, hakika zai gabatarwa majalisar dokokin kasar wannan bukata domin neman sahalewarta.

Karin bayani: Isra'ila ta gamu da fushin kasashen duniya a kan shirinta na Gaza

Bugu da kari firaministan ya bayyana cewa hatta a Ukraine ma, ta shirya bayar da irin wannan gudunmawa ta sojoji, don samar da zaman lafiya mai dorewa, bayan shafe shekaru hudu ana gwabza yaki tsakanin Ukraine din da makwabciyarta Rasha.

Spain na kan gaba cikin kasashen da ke sukar lamirin Isra'ila, kan farmakinta a Gaza, har ma a shekarar 2024 ta ayyana amincewarta da Falasdinu a matsayin 'yantacciyar kasa mai cin gashin kanta, lamarin da ya fusata Isra'ila sosai matuka.