SiyasaGabas ta Tsakiya
An kashe jagoran addinin Iran
March 1, 2026
Talla
Gidan talabijin na Iran ya tabbatar da mutuwar Ali Khamenei, inda rundunar juyin juya hali ta yi alƙawarin hukunci mai tsanani ga waɗanda suka aikata wannan aika-aika.
Kafafen yada labaran Iran sun kuma ruwaito mutuwar 'yar Jagoran, surukinsa, da kuma jikarsa.
Za a ci gaba da kai hare-haren bama-bamai a tsawon mako guda, in ji Donald Trump, wanda ya yi imanin cewa al'ummar Iran suna da mafi girman damar su kwaci iko da kasar, da wasu jiga-jigan mulkin na Iran.