Sojoji sun kwaci garin Abadam a Najeriya | Labarai | DW | 26.10.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sojoji sun kwaci garin Abadam a Najeriya

Duk da yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma, sojoji sun kwaci garin Abadam daga hannun 'yan Boko Haram bayan wani gumurzu na tsawon kwanaki biyu.

A cewar wani jami'in tsaron da bai so a bayyana sunansa ba, a halin yanzu garin na Abadam da ke kusa da tafkin Chadi cikin jihar Borno, ya kubuta daga hannun 'yan ta'adda, kuma sannu a hankali zasu ci gaba da karbar sauran garuruwan dake karkashin kulawar 'yan kungiyar. Mutanan wannan gari dai akasarin su sun tsere ne zuwa kasar Nijar tun lokacin da 'yan kungiyar ta Boko haram suka karbi ikon garin a ranar Juma'a 17 ga watan nan na Octoba.

Wannan majiya ta tabbatar wa kanfanin dillancin labaran kasar Faransa na AFP cewa, dakarun rundunar hadin gwiwa ce suka yi wannan aiki, da ta hada da sojojin Nijar, Chadi, Kamarun da kuma Najeriya, amma kuma babu wata majiya mai ta daban da ta tabbatar da wannan labari, kuma hakan na zuwa ne a dai dai lokacin da 'yan kungiyar suka yawaita kame-kaman yara kanana da suka hada da maza da mata, inda cikin kwanaki biyu 'yan kungiyar suka saci yara a kalla 30 a wajejan garin Mafa cikin jihar ta Borno.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Umaru Aliyu