Sojan Najeriya sun koma gida bayan buya a Nijar | Siyasa | DW | 10.11.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Sojan Najeriya sun koma gida bayan buya a Nijar

Tuni dai Jama'ar Diffa inda sojan Najeriya suka nemi mafaka a Jamhuriyar ta Nijar suka fada cikin halin zaman dar-dar sakamakon shigar dakarun sojan.


A karshen makon da ya gabata gwamnatin jihar Diffa da ke Jamhuriyar Niger ta mika daruruwan sojojin Tarayyar Najeriya zuwa ga gwamnatin kasar biyo bayan musayar wuta ta tsawon kimanin kwanaki uku tsakanin 'yan kungiyar Boko Haram da dakarun gwamnatin kasar a Malamfateri, hakan ya tilasta masu saranda a cewar wasu 'yan gudun hijirar da ke zaune a karamar Barikin Bosso da suka ganema idanun su yadda abun ya faru.

Tuni dai adadin 'yan gudun hijirar ya karu a ciki da wajen birnin jihar ta Diffa. Cikin mahukuntan Jihar ta Diffa babu wanda ya amince ya bada karin haske a kan wanan batu daga wanda baya daukan waya sai wanda zai ce baya gari sai kuma wanda wayoyinsu ke rufe. To amman a cewar wani ganau ba jiyau ba daga birnin na Diffa an hana jama'a shiga asibitin da ake kula da marasa lafiya da suka sami rauni a fafatawar.

Karo na biyu kenan bayan wanda suka fada Kamaru a guje tare da makamansu, ko da yake wancan karon sojojin Najeriyar sun ce basu da isasun kayan aiki, wanan karo basu yi magana da manema labarai ba.

Sauti da bidiyo akan labarin