Siyasar Najeriya ta dauki zafi | Siyasa | DW | 21.01.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Siyasar Najeriya ta dauki zafi

A Najeriya ana ci gaba da gangamin yakin neman zabe na 'yan takarar shugabancin kasar a zabe mai zuwa.

Jam'iyyun siyasa a Tarayyar Najeriya na ci gaba da yin zagayen jihohi a matsayin gangamin yakin neman zabe a zabukan da kasar za ta gudanar a watan Fabarairu mai zuwa. A wannan Laraba dai dan takarar shugabancin kasar a karkashin jam'iyya mai mulki ta PDP wanda kuma shine shugaban Tarayyar ta Najeriya wato Goodluck Ebele Jonathan ya je jihar Kano domin gudanar da yakin neman zaben kafin daga bisani ya wuce zuwa jigawa. Zuwan nasa domin kaddamar da yakin neman zaben nasa a Kanon da ke zaman birnin na biyu mafi girma a Tarayyar ta Najeriya na zwau ne kwana guda bayan da dan takarar babbar jam'iyyar adawa ta APC ya kai makamanciyar wanna ziyara a Kanon kana shima ya wuce jihar ta Jigawa. Zaben dai na zuwa ne a yayin da Najeriya ke tsaka da matsalar kalubalen rashin tsaro sakamakon hare-haren ta'addanci daga kungiyar Boko Haram da ke gwagwarmaya da makamai a kasar.

Sauti da bidiyo akan labarin