SIPRI: Cinikin makamai ya karu a Turai | Labarai | DW | 13.03.2023
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

SIPRI: Cinikin makamai ya karu a Turai

Cibiyar nazarin zaman lafiya SIPRI da ke Stockholm a rohoton da ta wallafa ta ce adadin makaman da ke shiga nahiyar Turai ya ninka a shekarar 2022.

Rahoton na SIPRI ya ce sakamakon yadda kasashen Turai ke tururuwar aike wa da makamai da tankokin yaki zuwa Kiev, Ukraine ta zama kasa ta uku inda aka fi shigar da makamai a duniya. Rohoton ya ce sabanin nahiyar Turai an samu raguwar cinikin makamai a sauran sassan duniya a shekaru biyar din da suka gabata.

Nahiyar Afirka ita ke kan gaba wajen rage sayen makamai da kashi 40%  sai Arewacin Amurka da 20% sannan nahiyar Asiya da kashi 7%  kana Gabas ta Tsakkiya da ke zama cibiyar hada-hadar makamai a can baya, inda a nan ma aka samu raguwa ta kashi 9% a cewar SIPRI. 

A bangaren masu kasuwancin makaman kuwa rahoton ya nunar da cewa Amurka ce ke kan gaba da kashi 40% yayin da Rasha ke bi mata da kashi 16%, sai Faransa a matsayi na uku da kashi 11%, Chaina a matsayi na hudu da kashi  5% sai kuma Jamus a matsayi na biyar da 4%.

Sai dai cibiyar ta SIPRI ta ce Amurka da Faransa sun kara adadin makaman da suke sayarwa yayin da aka samu raguwa a sauran kashen uku da ke biya masu.