Shugaban Sudan yayi gargadi game da aikewa da dakarun Majalisar Dinkin Duniya | Labarai | DW | 26.02.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaban Sudan yayi gargadi game da aikewa da dakarun Majalisar Dinkin Duniya

Shugaban kasar Sudan Omar al-Bashir ,yace yankin Darfur zai zama kabarin duk wasu dakarun kasashen ketare da suka shiga yankin ba tare da iznin gwamnatin kasar ba.

Wannan kalami na shi dai ya biyo bayan shiri ne na kasashen duniya su aika da dakarun Majalisar Dinkin Duniya zuwa Darfur domin hadewa da dakarun Kungiyar taraiyar Afrika(AU).

Al-Bashir ya kuma yi suka ga dakarun na AU da rashin nunwa adawa da maye gurbinsu da dakarun ma Majalisar Dibkin Duniya sukeyi.

Yace dakarun na AU zasu iya barin kasar Sudan,idan sunyi imanin cewa ba zasu iya gudanar da aikinsu na wanzar da zaman lafiya ba.