1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Shugaban Nijar Janar Tciani ya zanta da Putin

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
March 27, 2024

Ko a cikin watan Janairun da ya gabata kasashen biyu sun cimma yarjejeniyar tallafin tsaron, bayan da tawagar gwamnatin Nijar karkashin jagorancin firaminista Lamine Ali Zeine ta kai ziyara Moscow

https://p.dw.com/p/4e9vU
Hoto: ORTN/Télé Sahel/AFP/Getty Images

Shugaban mulkin sojin Jamhuriyar Nijar Janar Abdourahamane Tiani ya bayyana kokarin da kasarsa ke yi na kara yaukaka alakar tsaro da Rasha, bayan tattaunawa ta wayar tarho da shugaba Vladimir Putin na Rasha.

Karin bayani:Nijar: Ziyarar jami'an gwamnatin Rasha

Wata sanarwa da fadar gwamnatin kasar ta fitar, ta ce shugabannin biyu sun tattauna a ranar Talata, game da kalubalen tsaro da Nijar ke ci gaba da fuskanta, har ma da kasashen yankin Sahel, a wani mataki na dakile ayyukan ta'addanci.

Karin bayani:EU ta kama hanyar kakaba wa Nijar takunkumin karya arziki

Ko a cikin watan Janairun da ya gabata kasashen biyu sun cimma yarjejeniyar tallafin tsaron, bayan da tawagar gwamnatin Nijar karkashin jagorancin firaminista Lamine Ali Zeine ta kai ziyara Moscow.