Shugaban hukumar EU zai gana da Putin | Labarai | DW | 30.05.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaban hukumar EU zai gana da Putin

Shugaban hukumar Tarayyar Turai Jean-Claude Juncker zai gana da shugaban Rasha a karon farko bayan Rasha ta kwace yankin Kirimiya na Ukraine.

Babban jami'in kungiyar Tarayyar Turai, Jean-Claude Juncker zai gana da Shugaba Vladimir Putin na Rasha cikin watan mai kamawa na Yuni kamar yadda mai magana da yawun jami'in na Tarayyar ta Turai ya nunar.

Shugaban hukumar ta Turai Juncker zai zama babban jami'i na farko da ya gana da shugaban Rasha tun lokacin da kasashen Turai da Amirka suka dauki matakin kakaba wa Rasha takunkumi bayan da ta kwace yankin Kirimiya na Ukraine cikin shekara ta 2014.

Yayin taron manyan kasashe masu karfin arzikin masana'antu da ya gudana a Japan cikin makon jiya da shugaban hukumar ta Tarayyar Turai Jean-Claude Juncker ya halarta an amince da janye takunkumin da aka kakaba wa Rasha muddin ta aiwatar da yarjejeniyar da aka kulla a birnin Minsk na Belarus kan rikicin gabashin Ukraine.