1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaban gwamnatin Jamus Gerhard Schröder zai halarci bikin cika shekaru 60 da boren birnin Warsaw

Mohammad Nasiru Awal
July 30, 2004
https://p.dw.com/p/Bvhc
Tsofaffin sojojin Poland a birnin Warsaw
Tsofaffin sojojin Poland a birnin WarsawHoto: transit

Shugaba Lech Walesa na Poland ne ya gayyaci tsohon shugaban tarayyar Jamus Roman Herzog zuwa birnin Warsaw shekaru 10 da suka gabata. A ran daya ga watan agustan shekara ta 1994 lokacin da aka gudanar da bikin cika shekaru 50 da fara boren birnin Warsaw, shugaba Walesa ya yi amfani da wannan damar a matsayin wata alamar sansantawa tsakanin Poland da Jamus. To sai dai da yawa daga cikin al´umar kasar ba su ji dadin gayyatar da aka yiwa shugaban na Jamus ba. Dalili kuwa shine ba su manta da irin ta´asa da kuma cin zali da sojojin Nazi suka aikata akan mayakan rundunar Armia Krayowa wadanda ba su da isassun kayan yaki ba. Duk da haka dai tsohon shugaban na Jamus ya ziyarci yankin da sojojin Jamus suka murkushe ´yan tawaye kuma suka yi daya-daya da shi. Kafin ya yi wannan tafiya Mista Herzog ya fadawa tashar DW cewa:

"Muhimmin abu ne mu nuna zumunci tare da girmama wadanda suka ta da wannan bore na birnin Warsaw. A saboda haka a gare ni wannan gayyata abu ne da ta dace kuma in ke maraba da ita."

An dai shafe kwanaki 63 ana wannan bore a lokacin bazara na shekara ta 1944. Fadan da aka yi, yayi sanadiyar mutuwar mutane musamman ma fararen hula kimanin dubu 200 sannan wasu dubu 200 kuma aka tsugunar a sansanonin gwale-gwale bayan an murkushe boren. A jawabin da yayi a ran daya ga watan agustan shekarar 1994, shugaba Lech Walesa yayi tuni da wannan ta´asa da Jamusawa suka aikata akan mazauna birnin Warsaw, amma a lokaci daya ya mika hannun yin sulhu. Sannan ya kara da cewa ko da yake an zub da jinin wadanda ba su san hawa ba su san sauka ba, amma bai kamata a ci-gaba da zaman doya da manja tsakanin al´umomin Jamus da Poland, dole ne a yafewa juna don a samu zaman lafiya tsakanin kasashen makwabtan juna.

Shi kuwa a na shi jawabin, shugaba Herzog cewa yayi har abada Jamus zata ci-gaba da zama cikin kunya dangane da mummunar ta´asar da ta aikata akan ´yan Poland. Sannan sai ya kara da cewa:
"A yau ina mai sunkuyawa a gaban dukkan al´umar birnin Warsaw wadanda suka ta da wannan bore da kuma sauran al´umar kasar Poland da wannan yaki ya rutsa da su. Ina rokon gafara da abin da Jamusawa suka aikata akanku."

A duk fadin kasar ta Poland an yi maraba da rokon gafarar, wanda ke da muhimmanci a huldar dangantaka mai rauni da ta wanzu tsakanin Jamus da Poland tun bayan wannan yaki. A saboda haka gayyatar da aka yiwa shugaban gwamnati Gerhard Schröder don halartar bikin na bana, ba ta janyo kace-nace a Poland ba.