Shugaban Faransa na ziyarar farko a Jamus | Labarai | DW | 15.05.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaban Faransa na ziyarar farko a Jamus

Kwana daya bayan da ya soma aiki, sabon shugaban Faransa Emmanuel Macron ya soma wata ziyarar aiki a kasar Jamus, ziyarar da ke zama ta farko da ya kai a wata kasa tun bayan zabensa.

Emannuel Macron Angela Merkel Berlin (Reuters/F.Bensch)

Shugaban kasar faransa Emmanuel Macron da Shugabar Gwamnatin Jamus Angela Merkel lokacin da Macron ya kai ziyara a Jamus

Batun huldar dangantakar kasashen biyu musamman a game da manufofinsu kan kungiyar Tarayyar Turai ta EU, na daga cikin muhimman batutuwan da Shugaba Macron ya tattauna da Shugabar Gwamnatin Jamus Angela Merkel a lokacin ganawar da suka yi a birnin Berlin fadar gwamnatin kasar ta Jamus:

Kamar dai yadda shugaba Hollande da ya gaba ce shi ya yi shekaru biyar da suka gabta, shi ma dai sabon shugaban na Faransa Macron ya soma ziyararsa ta farko a kasar Jamus, inda ya ya samu babban tarbo daga Shugabar Gwamnatin ta Jamus Angela Merkel wacce ke cike da kwarin gwiwa dangane da makomar huldar dangantaka da ke tsakanin kasashen biyu, da kuma Tarayyar Turai. Sai dai a wannan ziyara babu wani batun jarjejeniyoyi da ake jira, amma kuma ana ganin shugabannin biyu ka iya duba wasu mahimman batutuwan da za su sa wa gaba.