A cikin shirin za a ji cewa ana ci gaba da mayar da martani kan matakin gwamnatin Najeriya na jingina filayen jiragen kasar hudu ciki har da Abuja ga 'yan kasuwa masu zaman kansu. A ranar 26 ga kowane watan Juni ne ake mutunta ranar da Majalisar Dinkin Duniya ta ware don yaki da safara da shaye-shayen miyagun kwayoyi.