A cikin shirin za a ji cewa Gwamnatin Najeriya na shirin bude tattaunawa da masu ruwa da tsaki cikin rikicin da ya hallaka rayuka a yankin Kudu maso gabashin da ke kallon sake tashin fatalwar Biafra. Dan takarar zaben shugabancin kasar Nijar ya garzaya kotun ECOWAS don kalubalantar zaben shugabancin kasar.