Yayin da Musulmi a duniya ke haramar fara azumin watan Ramadana, a Najeriya da Nijar jama'a na fama ne da matsalolin tsaro da annobar corona. Najeriya ta kaddamar da neman sama da mutane 3400 da suka tsere daga gidajen yari da ofisoshin 'yan sanda a kudancin kasar.