Muna amfani da "Cookies" domin inganta abubuwan da muke wallafawa a intanet. Za ku iya samun karin bayani a kundin kare bayananmu.
A cikin shirin za a ji cewar shugaban gwamnatin Jamus Angela Markel ta tattauna ta wayar tarho da zababben shugaban Amirka Joe Biden inda ta taya shi murna da kuma jaddada kudirin karfafa hulda tsakanin nahiyar Turai da Amirka.
An shirya shugabannin biyu za su tattauna batun kara ba da makamai ga Ukraine wadanda suka hada da tankokin yaki masu sulke.
Shugaban Amurka Joe Biden ya ce janyewar da Rasha ta yi daga cikin yarjejeniyar kawar da makaman nukiliya ta New Start wani babban kuskure ne.
Shugaba Joe Biden ya nemi duk bangarorin da ke tayar da jijiyoyin wuya a Ireland ta Arewa da su daidaita tsakaninsu gudun mayar da hannun agogo baya.
Tsohuwar shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta karbi lambar yabo mafi girma ta kasa a wannan Litinin duk da sukar lamirin da ake yi na ayyukan da ta yi a zamanin mulkinta musamman manufofinta a kan Rasha.