Muna amfani da "Cookies" domin inganta abubuwan da muke wallafawa a intanet. Za ku iya samun karin bayani a kundin kare bayananmu.
A cikin shirin za a ji cewa Kotun koli a Najeriya ta ba da umarnin ci gaba da amfani da tsoffin kudin Naira har nan da karshen shekarar 2023. 'Yan Nijar na cike da fatan ganin sabuwar gwamnatin Najeriya ta inganta hulda a tsakanin kasashen biyu.
Gwamnatin Najeriya ta bayyana damuwa a kan yaduwar kananan makamai a tsakanin jama'a ganin yadda hakan ya ke da illa musamman ga mata da kananan yara.
Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya, ya kaddamar da matatar man fetur ta Dangote a Ijebu Lekki a birnin Legas, matatar da ke iya sama wa sama da mutum dubu 100 aikin yi.
Mabiya addnin Kirista a fadin duniya na gudanar da bukukuwan Kirsimeti da suka saba gudanarwa duk shekara, a wani mataki na tunawa da Yesu Al-masihu.
A wannan Litinin aka bude babban taron kasa da kasa a birnin Yamai na kasar Nijar don nazari kan yadda za a sake gina yankin Tafkin Chadi da rikicin Boko Haram ya daidaita.