A cikin shirin za a ji cewa wasu da ake kyautata zaton mayakan kungiyar ISWAP ne, sun yi garkuwa da ma'aikatan gwamnatin shida a jihar Borno da ke yankin Arewa maso gabashin Najeriya. A yayin da ake wannan su kuwa kungiyoyin mata taron gangami suka yi, da zummar nuna rashin jin dadinsu kan halin da kasar Najeriya ta fada ciki na tabarbarewar tsaro.