1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shekaru 40 da kulla huldar diplomasiyyar Jamus da Isra'ila

May 12, 2005

A daidai ranar 12 ga watan mayun shekarar 1965 ne aka yi bikin kulla dangantakar diplomasiyya tsakanin Jamus da Isra'ila bayan samun shekaru 20 da ta'asar kisan kiyashi akan Yahudawa a nahiyar Turai

https://p.dw.com/p/Bvc2

Shin kuwa Ya-Allah watan-wata rana za a wayi gari inda al’amura zasu daidaita ba tare da wata kura ba a dangantaka tsakanin Jamus da Isra’ila? Da wannan ayar tambaya Peter Philipp ya fara sharhinsa inda ya ci gaba da cewar:

A cikin shekaru arba’in din da suka wuce, bayan kulla dangantakar diplomasiyyar tsakanin Jamus da Isra’ila an sha gudanar da mahawarori a game da lokaci da kuma hanyoyin da za’a bi al’amura su daidaita ba tare da wata kura ba a huldodi tsakanin kasashen biyu. Jamus ce ta fara neman ganin an daidaita huldodinsu, amma Isra’ila ta ki yarda da haka saboda tabon da take fama da shi daga ta’asar kisan kiyashin da aka yi wa Yahudawa a nahiyar Turai. A sakamakon haka Jamus ta hakura tana mai kwatanta dangantakar tamkar wata manufa ta musamman. To sai dai kuma wani abin mamaki shi ne a yayinda a nan Jamus ake ba da la’akari sosai da sosai game da zagayowar wannan rana ta samun shekaru 40 da kulla dangantakar tsakanin kasashen biyu, a can Isra’ila watsi aka yi da lamarin. Mai yiwuwa bisa ga ra’ayin Isra’ilawan tuni dangantakar ta zama ta al’ada kuma wani bangare na manufofin ketare na kasarsu, a saboda haka babu wani dalili na doki da murna game da shi. Amma a fakaice ba haka lamarin yake ba. Yahudawan Isra’ila har kwanan gobe ba zasu manta da ta’asar ta kisan kiyashin da ‚yan Nazinhitler suka yi musu a nan Jamus da sauran sassa na nahiyar Turai ba. Sai dai kuma duk da haka lokaci yayi da za a rika nakaltar al’amura a zahirinsu domin samun ci gaba a rayuwa. Ita dai Jamus, daya daga cikin dalilan da suka sanya ta dage wajen ganin lalle sai ta kulla dangantakar diplomasiyya da Isra’ila a wancan lokaci, shi ne domin ta samu karbuwa a tsakanin sauran kasashe. Daga baya wannan dangantakar ta dauki wani sabon fasali mai muhimmanci, saboda an wayi gari Isra’ila ta zama gida ga Yahudawa masu tarin yawa da suka tsira daga ta’asar ta kisan kiyashi, a tsakaninsu kuwa akwai Yahudawa da dama da suka fito daga Jamus. Wani abin lura kuma shi ne wannan dangantaka ta diplomasiyya da Jamus ta kulla da Isra’ila ta shafa wa kasar kashin kaza a tsakanin kasashen Larabawa, wadanda suka yi watsi da tarihin ta’asar, suka kuma dauka cewar goyan bayan da Jamus ke ba wa Isra’ila wani mataki ne na adawa da Larabawa. Sai da ya dauki lokaci mai tsawo kafin kasashen na Larabawa su kai ganon cewar goyan bayan ga Isra’ila ba ta ma’anar adawa da su. Amma fa goyan bayan ya shafi mutanen da ta’asar ‚yan Nazinhitler ta rutsa dasu ne, ba dukkan Yahudawan Isra’ila ko wasu manufofi na gwamnatin kasar ba. Tilas ne a sake ba wa dangantakar Jamus da Isra’ila wani sabon fasalin da ya dace, saboda sannu a hankali masu alhakin ta’asar a nan Jamus da kuma wadanda ta rutsa da su a Isra’ila, suna mutuwa kuma matsalar tuni ta zama ta tarihi. Da yawa daga al’umar Isra’ila sun fahimci haka. Mai yiwuwa nan gaba Jamusawan su samu wata cikakkiyar kafa ta gudanar da hutunsu a wannan kasa. Dangane da batutuwan siyasa kuwa Jamus ce kadai ke da ikon murkushe wariyar jinsi da zazzafan ra’ayin kyamar baki a kasar, ba ta bukatar taimako daga Isra’ila.