Shekaru 100 ga dangantakar Jamus da Habasha | Siyasa | DW | 07.03.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Shekaru 100 ga dangantakar Jamus da Habasha

A yau litinin ake bikin samun shekaru da kulla dangantakar kawance da ciniki tsakanin Jamus da Habasha a daidai ranar 7 ga watan maris na 1905

Kasar Habasha dai ita ce ta biyu a tsakanin kasashen Afurka da suka fi yawan jama'a tare da al'umarta kimanin miliyan 70 ko da yake tana daga cikin rukunin kasashe masu tasowa, wadanda ba su da ci gaba na a zo a gani. A sakamakon haka aka fi ba da la’akari ga manufofin taimakon raya kasa a dangantakar kasar da kasar Jamus. Dangantakar kasashen biyu dake da tarihin kimanin shekaru 100 tana tafiya salin alin ba tare da wata tangarda ba, musamman ma a bangaren al’adu, lamarin da ya sanya aka shigar da harshen mutanen Habasha a cikin jerin harsunan Afuurka guda uku da tashar Deutsche Welle ke yada shirye-shiryenta a cikinsu, wato a baya ga Hausa da Kiswahili. Kazalika a daura da cibiyar al’adu ta Goethe dake da reshenta a Addis Ababa, akwai kuma wata makaranta ta Jamusawa a wannan birni, wanda mutanen Habasha ke kwatanta shi tamkar fadar mulkin Afurka saboda kasancewar shelkwatar kungiyar tarayyar Afurka AU a cikinsa. Tun a cikin shekarun 1960 Kungiyar Taimakon Fasaha ta Jamus GTZ a takaice take tafiyar da shirye-shiryen rayawa masu tarin yawa a kasar ta Habasha sai kuma wasu kungiyoyin tamakon jinkai masu zaman kansu, kamar kungiyar taimakon abinci ta Jamus Welthungerhilfe, dake gudanar da ayyukansu a kasar ta gabacin Afurka dake da muhimmanci ta fuskar tsaro. An saurara daga bakin jakadiyar Jamus a Habasha Helga Gräfin tana mai bayanin cewar ko da yake ba za a rasa dan sabani ba, amma al’amuran sun tafi salin alin tun bayan kulla yarjejeniyar kawance da ciniki da aka yi tsakanin Jamus da Habasha a daidai ranar bakwai ga watan maris na shekara ta 1905. Misali an samu sararawar dangantakar a lokacin yakin duniya na biyu da kuma lokacin yaki tsakanin Habasha da Eritrea, saboda Jamus ta bayyana adawarta da wanzuwar yaki a shiyyar. Amma tuni aka dinke wannan baraka, inda a shekarar da ta wuce shugaban gwamnatin Jamus Gerhard Schröder ya kai ziyara Addis Ababa sannan shi kuma P/M Meles Zenawi ya rama wannan ziyara a cikin watan nuwamban bara, kafin shi kuma shugaban kasar Jamus Jürgen Köhler ya sake ya da zango a fadar mulki ta Addis Ababa a cikin watan desamban bara. A lokacin wannan ziyarar ce aka yafe wa Habasha bashin Euro miliyan 67 da Jamus ke binta, ta yadda kasar zata samu kafar tinkarar matsalarta ta talauci. A kuma cikin watan nan na maris za a gabatar da shawarwari a Berlin akan wani matakin taimakon raya kasa dangane da shekaru uku masu zuwa, inda za a duba hanyoyin da zasu taimaka wajen kyautata ayyukan samar da abinci ta la’akari da barazanar fari da kasar ta dade tana fuskanta.