Sanyi ya tsananta a Turai | Labarai | DW | 20.01.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sanyi ya tsananta a Turai

Daskarewar dusar kankara ta janyo tsantsi mai hadarin gaske da kuma tarnaki ga harkokin rayuwa a wasu yankuna na nahiyar Turai.

A dalilin hakan ne ma aka toshe wasu hanyoyi a kudanci da kudu maso yammacin Jamus. Hakan ta tilasta wa mutane da dama saura a gidjensu saboda tsaron fuskantar hadari sakamakon daskarewar da dussar kankara akan hanyoyin mota da na kafa. A filin saukar jiragen sama Frankfurt da ke Jamus an soke tashin jirage sama da 130 na fsinjojin da ke son karasawa zuwa gaba. A Filin sukar jiragen Stuttgart kuwa an soke tashi dasaukar jirage ga baki daya. Ana kuma fuskantar cikas a tashar jiragen saman Heathrow na birnin London sakamakon zubar dussan kankara- dalilin da ya sa aka soke tashin jirage 260. Ga baki daya kuma an dakatar da zirg- zirgar jiragen kasa da motoci a fadin Birtaniya. A Northern Ireland kuwa ana fuskantar katserwar wutar lantarki. Hakazalika al'umar Faransa su kuma suna shan fama sakamakon daskarewar dusar kankara-abin da ya janyo dakatar da tashin kashi 40 daga cikin dari na jiragen sama a filayen saukarsuu na Charles de Gaulle da Orly da ke birnin Paris.

Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Usman Shehu Usman