Rundunar sojin Amurka ta karyata cewa ta kai hari a masallacin yan shia | Labarai | DW | 27.03.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rundunar sojin Amurka ta karyata cewa ta kai hari a masallacin yan shia

Rundunar sojin Amurka ta sanar da cewa,ba sojojinta bane suke da alhakin kai hari kann wani masallacin yan shia a arewa maso gabashin Bagadaza inda akalla mutane 16 suka rasa rayukansu,rundunar tace sojojin Iraqin ne suka kai wannan hari.

A daren jiya lahadi gidan telebijin na Iraqi ya nuna hotunan wadannan mutane jina jana a cikinn wani masallaci,wadanda akayi harin akan idanunsu sunce sojojin Amurka ne suka kashe wadannan mutane.

Tun farko yan sanda na Iraqin sun bada rahoton cewa,sojin Amurka sunyi musayar wuta da magoya bayan Muqtada As Sadr a wannan yanki.

Rahotanni daga kasar Iraqin kuma sunce,yan sanda sun gano gawarwakin wasu 12 a yau,a jiya ne dai aka gano wasu kuma mutane 30 da aka yankewa kawunansu,kusa da garin Baquba,a wajen Bagadaza.

An dai gano gawarwakin daruruwan mutane a Iraqi,tun bayan hari da aka kai a wani masallacin yan shia a Samarra a watan daya gabata,wanda ya kusa jefa kasar cikin yakin basasa.