Rikicin jam′iyyar APC a jihar Rivers | Labarai | DW | 15.08.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rikicin jam'iyyar APC a jihar Rivers

Wata sabuwar rigima ta barke a Jam'iyyar APC a Jihar Rivers tsakanin bangaren Minista Rotimi Amechi da na Sanata Magnus Abbe bangarori biyu da ke gaba da juna.

A halin da ake ciki kamar yadda wakilinmu na yankin Niger Delta Muhammad Bello ya ruwaito mana, an aike da jami'an tsaro domin shawo kan wannan arangama, da ta hada har da harbe harben bindigogi da harba barkonon tsohuwa.

Arangamar da ta faru a babban ofishin jamiyyar na Jiha da ke kan Aba road kusa da Garrison, na zaman arangama ta biyu a cikin mako daya a jihar. Sai dai kokarin wakilin namu na jin ta bakin rundunar 'yan sandan jihar kan wannan batu ya ci tura.