Rikici a Najeriya ya ki ci ya ki cinyewa | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 23.05.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Rikici a Najeriya ya ki ci ya ki cinyewa

Ayyukan tarzoma na Boko Haram a Najeriya da kuma gazawar mahukunta na kawo karshen su, su ne suka dauki hankalin jaridun na Jamus a wannan mako.

A lokacin da take tsokaci game da aika-aikar kungiyar ta Boko Haram jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung cewa ta yi ayyukan ta'addancin wannan kungiya sun ki kawo karshe inda a wannan makon ta kai hare-haren bam a biranen Kano da Jos da suka yi sanadiyyar mutuwar mutane da yawa, baya ga kashe wasu mutanen da 'ya'yan kungiyar suka yi a arewa maso gabacin Najeriya, tare kuma da kona gidaje a kauyukan jihar Borno. Wannan aika-aikar nuna karfi ne da masu ta da kayar bayan ke yi tare da kuma kunyata gwamnatin shugaban kasa Goodluck Jonathan wadda ta gaza kawo karshen wannan ta'asa. Kuma duk da tsawaita dokar ta-baci a jihohin Borno, Yobe da Adamawa, har wayau kungiyar na cin karenta babu babbaka a wannan yanki.

Tarzoma a Najeriya da sabuwar manufar Jamus a Afirka

Yaki da Boko Haram a kan takarda, inji jaridar Die Tageszeitung a cikin sharhin da ta rubuta tana mai mayar da hankali a kan tarzoma a Najeriya da kuma sauyin manufar tarayyar Jamus game da nahiyar Afirka.

A martanin da ta mayar bayan gwamnatin Najeriya ta yi shailar yin yaki gada-gadan da ita, Boko Haram ta kai hare-hare mafi muni a cikin tarihinta. Wannan zai kara jefa gwamnatin Najeriya da kawayenta cikin rashin tabbas bisa ga matakan sojin da suke dauka. Wannan dai na faruwa ne a daidai lokacin da gwamnatin tarayyar Jamus ta amince da sabuwar manufa game da nahiyar Afirka da ke da zumar karfafa shigar da kasar cikin ayyukan magance rikice-rikice a Afirka. Sai dai sanin kowane Jamus ba za ta daga wa Boko Haram yatsa ba. Wannan aiki ne da ke kan Birtaniya a matsayin tsohuwar 'yar mulkin mallaka da Faransa a matsayin 'yar kutse da kuma Amirka da ke matsayin babbar kawar Najeriya. Ga Najeriya, Jamus na da muhimmanci ne a fannin aikin gine-gine, injuna da motoci wadda kuma 'yan siyasar Najeriya da ba su da lafiya ke shigowa don neman magani. Shin me Jamus ke so kuma me za ta iya yi? Ba amsa ga wadannan tambayoyin. Yanzu Najeriya mafi yawan al'umma a Afirka na fuskantar wani yaki wanda ya mayar da rikicin janhuriyar Afirka ta Tsakiya tamkar wani wasan yara.

Tsugune ba ta kare ba a arewacin Mali

Daga rikicin Najeriya sai na Mali inda jaridar Süddeutsche Zeitung ta labarto cewa kasar Faransa ta dakatar da shirin janye dakarunta daga Mali biyo bayan musayar wuta da kashe kashen da aka yi a karshen mako da kuma a tsakiyar mako a Kidal da ke arewacin Mali. Da farko dai Faransa ta so janye sojojinta daga Mali ta tsugunar da su a wasu wuraren da ake fama da rikici a Afirka. Daga cikin sojoji 5000 da Faransa ta girke don maido da zababbiyar gwamnatin Mali a shekarar 2012 yanzu haka saura 2000 a cikin kasar. Kuma Faransar ta so rage yawansu da 1000, to amma ta dakatar da wannan shirin, abin da kuma a cewar jaridar ta Süddeutsche Zeitung na zaman rage nauyi ga rundunar sojin Jamus da a nata bangaren ta so girke sojoji fiye da 200 a Mali karkashin inuwar tarayyar Turai da kuma Majalisar Dinkin Duniya.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Usman Shehu Usman