Rice ta kai ziyarar ba zata a Bagadaza | Labarai | DW | 05.10.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rice ta kai ziyarar ba zata a Bagadaza

Sakatariyar harkokin wajen amurka Condoleeza Rice ta kai wata ziyara ba zata zuwa birnin Bagadaza,bayan ganawarta da shugabanin Israila a yau din,a ci gaba da ziyarata zuwa yankin gabas ta tsakiya.

Rice ta gana da firaministan Iraqi Nuri al-Maliki kana ta tattauna da jamian Amurka da na Iraqin,a kokarinda kasar Amurkan take yi na na ganin an lafarda tashe tashen hankula dake kara muni a kasar.

Rice tace aikinsu shine su bada goyon baya ga dukkan bangarori tare da matsa masu lamba suyi aiki tare wajen gaggauta nemo bakin zaren warware rikicin kasar,saboda a cewarta a fili yake cewa ba zaa zuba ido ana ganin halinda tsaron kasar yake ciki ba tare da taimaka ba.

Tun ziyara Rice ta karshe a watan Afrliu kasar Iraqi ta sake fadawa cikin tashe tashen hakula da suke sanadiyar rayukan mutane fiye da 100 a kowace rana.

Yanzu haka dai yawan dakarun Amurka a Iraqi ya karu daga 132,000 zuwa 142,000.