Pakistan ta fusata game da farmakin da Amirka ta kai akan wani kauyen kasar | Labarai | DW | 14.01.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Pakistan ta fusata game da farmakin da Amirka ta kai akan wani kauyen kasar

Pakistan ta mika takardar nuna fushinta a hukumance ga ofishin jakadancin Amirka dangane da mutuwar ´yan kasar su akalla 18 a wani farmakin da jiragen saman yakin Amirka suka kai da nufin halaka mataimakin shugabab kungyiar al-Qaida Ayman al-Zawahiri. Jami´an Pakistan dake gudanar da binciken don gano ko an halaka na hannun damar Osama Bin Laden a wannan farmaki, sun ce bai mai yiwuwa ba ne al-Zawahiri na cikin kauyen na Pakistan a lokacin da aka kai harin. Kafofin yada labarun Amirka sun rawaito wasu jami´an leken asiri na cewa an auna wannan hari ne akan al-Zawahiri. To amma mazauna yankin sun ce dukkan wadanda aka kashe a harin ´yan kabilar yankin ne kuma daukacinsu mata ne da kananan yara. A yau mutane kimanin dubu 5 sun gudanar da taron gangami a filin wasan yankin Bajur don yin Allah wadai da harin.