Obama da Merkel sun halarci taron Furotestan | Siyasa | DW | 25.05.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Obama da Merkel sun halarci taron Furotestan

Kiristoci mabiya darikar Furotestan sun halarci taronsu da ke zama na 500 da aka shirya a Berlin na Jamus. Muhimman batutuwa da ake mayar da hankali a kansu sun hada da matsalar 'yan gudun hijira da yake-yake a duniya.

Fitattu daga cikin mahalarta taron kimanin dubu 140 dai shi ne tsohon shugaban Amirka Barack Obama, wanda ya yi jawabi dangane da muhimmancin nauye-nauyen da suka rataya a wuyan jama'a, tare da diyar Pastor kuma shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel. Sakon dai na kai tsaye ne da ke bayyana cewar, dimukaradiyya na bukatar adalaci da yarda da manufofin mahalicci, da mutane da kan iya yayata irin wadannan sakonni kamar Obama.

Taron na bana dai zai kunshi bukukuwa guda 2,500, da masu bada gudunmowa da baki dubu 30 daga sassa daban-daban na duniya, da zasu yi muhawara kan gyare-gyare da al'adar mabiya darikar ta Furotestan.

Rev Dr Yusuf Ibrahim Wushishi, shi ne babban sakataren majalisar mabiya addinin Kirista a Najeriya, kuma daya daga cikin mahalarta taron na Berlin. Babban taron wanda ake gudarwa bayan shekaru biyu tun daga 1949, taro ne na kasa da kasa, a lokaci guda kuma a tsarin buki irin na Jamus.

Reinold von Thadden-Trieglaff (picture-alliance/dpa)

Dan siyasa daga gabashin Jamus Reinold von Thadden ne ya kirkiro taron Furotestan

 

Dan siyasa daga gabashi Reinold von Thadden, kuma mamber na majami'ar darikar Furotestan ya kirkiro taron saboda adawarsa da gwamnatin Nazi a wancan lokacin. Von Thadden ya kasance mai sukar akidojin 'yan Nazi, kana daga bisani ya kasance shugaban wannan zauren mashawarta har ya zuwa shekara ta 1964.

Sirkka Jendis ita ce kakakin darikar Protestant. Ta ce " A  shekarun baya majami'ar Furotestanbasta taka wata rawa cikin gwamnatin wancan lokaci mai ra'ayin gurguzu,  hakan ne ya tilastasu kirkiro zauren taron mabiya darikar da kawo yau ake kira "Kirchentag" a nan Jamus.  Kuma ya samu amincewa daga bangaren gwamnati saboda tsawon lokaci mabiya darikar Katolik ke gudanar da taro makamancin wannan".

Tsawon shekaru dai wannan zauren taro ya samu bunkasa daga na cikin gida zuwa na kasa da kasa. Kuma taron na bana zai tattauna muhimman batutuwa da suka addabi duniya kama daga matsalar 'yan gudun hijira , yake-yake,  hakuri da ma cudanya tsakanin mabiya dariku da addinai. 

Deutschland 36. Evangelischer Kirchentag in Berlin (picture-alliance/dpa/M. Gambarini)

Mutane dubu 140 ne suka halarci taron mabiya darikar Furotestan a Berlin

Mahalarta taron daga Afirka a nasu bangaren za su yi kokarin fahimtar da takwarorinsu da ke wannan bangaren duniya  zahirin abin da al'ummar nahiyar ke ciki, musamman batutuwa na yaki da 'yunwa da kalubalantar matsalolin tsaro kamar yadda Reverend Wushishi ya nunar.

Saura mahalarta wannan babban taro sun kunshi Archbishop na Cape Town a Afirka ta Kudu Thabo Makgoba, da babban limamin masallacin Al-Azhar da ke birnin Alkahiran Masar Sheik Ahmed el-Tayyib, da fitacciyar mai hannu da shuni kuma tsohuwar matar Bill Gates watau Melinda Gates da manzon MDD Staffan de Mistura.

Sauti da bidiyo akan labarin