Nigeria ta shiga zaman jana´iza na kwanaki ukku | Labarai | DW | 24.10.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Nigeria ta shiga zaman jana´iza na kwanaki ukku

Yau ne a taraya Nigeria a ke fara zaman jana´iza na kwanaki 3, a sakamakon hadarin jirgin sama,na kampanin Bellview Airlines da ya hadasa mutuwar mutane 117, ranar asabar da ta wuce.

Sanarwar da gwamnatin taraya ta bayyana, ta gayyaci jamaá da ta gudanar da adduóí ga wanda Allah ya ma cikawa cikin wanan mumuna hadari.

Haka zalika za a sassabto tutocin kasar har tsawon kwanaki 3, domin nuna karamci da tawsayawa ga mattatun.

Sannan shugaba Olesegun Obasanjo, da bugu da kari ke cikin zaman makomin matar sa da Allah yayi wa cikawa jiya, ya bayyana dakatar da duk alkawuran ayyukan da ya dauka, daga yau zuwa gobe, inji kakakin padar shugaban kasa Remi Oyo.

Komishinan yan sanda na jihar Ogun,Tunji Alapini, inda hadarin jirgin ya wakana, yace an samu akwatinan jirgin masu rijistan dukkan abubuwan da ke wakana.

Kurraru ta fannin ayyukan jiragen sama za su gudanar da bincike domin gano mussabbabin hadarin.