Najeriya za ta jagoranci yaki da Boko Haram | Labarai | DW | 03.06.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Najeriya za ta jagoranci yaki da Boko Haram

An nada wani Janar dan Najeriya ya jagoranci rundunar kasa da kasa da ke yaki da kungiyar Boko Haram.

Najeriya ta bayyana sunan wani hafsan sojinta da zai jagoranci rundunar kasa da kasa da ke yaki da kungiyar Boka Haram. Yanzu Najeriya za ta karbi ragamar daga hannun kasar Chadi. Wannan nadin ya zo ne kwana guda gabanin ziyarar aikin da sabon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai kai birnin N'Djamena da kuma shalkwatar rundunar a ranar Alhamis. Wata sanarwa daga ma'aikatar tsaron Najeriya ta ce tuni Manjo-Janar Tukur Yusuf Buratai ya fara sabon aikinsa na jagorantar dakarun daga Najeriya da Chadi da Kamaru da kuma Nijar. A wannan Laraba shugaban na Najeriya ya kai ziyarar aikinsa ta farko a Nijar, inda ya tattauna da shugabannin kasar game da rikicin na Boko Haram.