Najeriya: Kotu ta kori karar Atiku | Labarai | DW | 11.09.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Najeriya: Kotu ta kori karar Atiku

A Najeriya, kotun sauraron korafe-korafen zabe, ta yi watsi da karar da dan takarar shugabancin kasar a karkashin babbar jam'iyyar adawa ta PDP Atiku Abubakar ya shigar gabanta.

Muhammadu Buhari und Atiku Abubakar

Shugaban Najeriya Muhammadu Buharida dan takarar jam'iyyar adawa Atiku Abubakar

Atiku Abubakar dai ya nemi kotun ta soke zaben shugaban kasar da ya bai wa Shugaba Muhammadu Buhari nasara. Abubakar da ya taba kasancewa mataimakin shugaban kasa, a yayin mulkin stohon shugaban kasar Olusegun Obasanjo ya kalubalanci zaben ne bisa zargin an tabka magudi. Da wannan hukuncin na kotu, ya tabbata cewa Shugaba Muhammadu Buhari ne ya lashe zaben shugaban kasar da aka gudanar cikin watan Fabarairun wannan shekarar. Buhari da ke da shekaru 76 a duniya ya kasance tsohon shugaban mulkin soja a Najeriyar, ya kuma dare kan karagar mulki a karkashin gwamnatin dimukuradiyya a shekara ta 2015 a wa'adi na farko, kafin ya sake tsayawa takara a wannan shekarar inda ya sake lashe zaben da ke cike da tababa.