Najeriya: Karin kudin fito don bunkasa masana'antu
January 5, 2017Talla
Gwamnatin Najeriya ta yi karin kudin fito da wasu kayayyaki na jin dadi da motoci tare da rage kudin da ake biya a kan kayayyakin masana’antu a mataki na taimaka farfado da masana’antu na cikin gida da sanya al’umma amfani da kayayyakin da ake samu a kasar maimakon dogaro da na kasashen waje.