Najeriya na ba da fifiko ga kayayyaki na cikin gida | BATUTUWA | DW | 03.01.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

BATUTUWA

Najeriya na ba da fifiko ga kayayyaki na cikin gida

Gwamnatin Najeriya ta yi karin kudin fiton wasu kayayyaki na jin dadi da motoci tare da rage kudin da ake biya a kan kayayyakin masana’antu a mataki neman farfado da masana’antu na cikin gida.

Gwamnatin Najeriya ta yi karin kudin fito da wasu kayayyaki na jin dadi da motoci tare da rage kudin da ake biya a kan kayayyakin masana’antu a mataki na taimaka farfado da masana’antu na cikin gida da sanya al’umma amfani da kayayyakin da ake samu a kasar maimakon dogaro da na kasashen waje.

Karin kudin fiton da aka yi na kayayyakin, ya fi shafar manyan motoci na kawa da wadanda masu hannun da shuni ke shigowa da su kasar, da barasa, da ma taba sigari da ta samu kari daga kashi 20 zuwa 60 cikin dari. 
Matakin da ya biyo bayan fara amfani da tsarin hana shiga da motoci ta kan iyakokin Najeriya na kasa sai dai ta teku, ya nuna cewa motocin da ba sababi ba na Tokumbo sun samu kari zuwa kashi 35 cikin dari na kudin harajin da ake biya masu farkon shiga da su Najeriyar, abin da ya sanya shugaban kungiyar masu sayar da motoci a Najeriya Prince Ajibola Adedoyin ya bayyana yadda suke kallon mataki da cewa yana bukatar gyara:

Nigeria Unruhen und Landwirtschaft (AFP/Getty Images)

Bunkasa aikin noma a Najeriya domin daina shigo da kayan abinci daga waje

‘’Wannan dokar babu yadda za’a yi ba za ta shafi rayuwar mutane ba, domin kudin mota zai karu domin an kara kudin fito tun kafin ma a kara kudin haraji na shigo da motoci bale a yanzu, kafin wannan lokaci ai membobinmu da suka bar kasuwar nan za su kai dubu 800, a yanzu kuma abin zai karu. Ba wai muna cewa manufar ba ta da kyau ba ne, amma abin da muke so a dauki lamarin mataki mataki don muma muna son ganin Najeriya ta dogara da kanta’’

 

Ana dai kallon matakin a matsayin hanya ta samun karin kudadden shiga ga gwamnatin Najeriyar musamman ta hanyar hukumar kula da shigi da ficin kayayyaki da matsaloli na fasa kwauri da ma karkatar da kayan zuwa kasashen makwafta irin na Jamhuriyar Benin da Togo ya haifar a da koma baya ga Najeriyar. Mr Samuel Attah shi ne kakakin hukumar ta kwastom a Najeriya, ya bayyana cewa  ba wani sabon abu ba ne a kan batun harajin da ake magana:


‘’Ai abin da muke karba na shigo da mota shi ne kashi 35 wanda a a yanzu sai ta ruwa ake shigo da su, shinkafa kuma ai akwai bambanci domin ga wanda ba ya da masana’antar sarrafata daban ne da masu ita daga kashi 10 ne har zuwa kashi 60"


ARCHIVBILD Nigeria Norden Flucht (imago stock&people)

Kara kudin fiton shigo da motocin tuwaris a Najeriya

Kokarin na bunkasa kayan da ake samu a cikin Najeriyar rin su shinkafa da tuni gwamnati ta dauki mataki na a nomata a cikin kasar da aka fara ganin faraga daga hakan, da siminti da Najeriyar ke da albarka ta arzikinsa a cikin kasar da ma sauran kayayyaki da ba su zama dole ba.
Abin da ya yiwa masu masana’antu kyawo shi ne rage kudin haraji na kayyakin da masana’antu ke amfani da su a cikin kasar zuwa kasha biyar cikin 100 domin taimaka bunkasa masana’antun Najeriyar da mafi yawansu suka durkushe saboda tsadar kayayyakin da suke shigowa da su da ma matsala ta rashin wutar lantarki. Malam Ali Butu wani mai harkar masana’antu ya bayyana cewa shirin zai matukar tasiri ga farfado da masana'antu a kasar.
Matakan da gwamnatin Najeriyar ke dauka a kan shigo da kaya kasar sun kasance wadanda ake wa kallo ta fuskar rage dogaro da shigo da kayayyaki daga kasashen ketare da ta haramta wasu da dama, duk da korafi na matsin da wannan ke haifarwa, kwararu na masu cewa wannan ce mafita ga makomar kasar  muddin tana son samun ci gaba.

Sauti da bidiyo akan labarin