1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ministan wajen Jamus ya kai ziyara Libya

June 11, 2007
https://p.dw.com/p/BuJC

Ministan harkokin wajen Jamus Frank Walter Steinmeier ya gana da wasu masu dauke da cutar AIDS da kuma maaikatan jiyyan nan 5 yan kasar Bulagari da asuke fuskantar hukuncin kisa a kasar Libya,wadanda kuma Kungiyar Taraiyar Turai take neman a sako su.

Su dai wadannan maaikatan jiyya sun karyata wannan zargi suna masu baiyana cewa tun farko sun amince ne saboda azabtar dasu da akayi.

Kwarraru na kasashen ketare a nasu bangare sun dora laifin kann rashin kyakyawar tsabta.

Steinmeier dake wakiltar KTT wanda ya isa Libya tare da komishinar hulda da kasashen ketare ta KTT Benita Ferrero waldner,yace kasashen turai suna taimaka rage wahalhalu da yan da suka kamu da cutar suke ciki haka kuma suna kokarin ganin an sako wadannan jamian kula da lafiyar.

Ana sa ran steinmeier zai gana da shugaban kasar ta Libya Muammar Ghaddafi domin tattauna wannan batu.