Miliyoyin mutane a sassan duniya na cigaba da bukukuwan sabuwar shekara | Labarai | DW | 01.01.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Miliyoyin mutane a sassan duniya na cigaba da bukukuwan sabuwar shekara

New Year/World

Miliyoyin jamaa a biranen duniya daban daban na cigaba da bukukuwan shigowar sabuwar shekarar miladiyya ta dubu biyu da shida.

Anan Jamus miliyoyin mutane ne suka tattaru a kofar Brandenburg dake birnin Berlin domin bikin shigowar sabuwar shekarar da kuma murnar farkon shekarar da za a gudanar da wasan cin kofin duniya na kwallon kafa da za ayi a kasar.

A kasar faransa kuwa yayinda dubun dubatar masu murnar shigowar sabuwar shekarar ke shagulgula a dandalin nan na Champs Elysees dake Paris can kuma a wasu garuruwan wajen birnin na Paris masu tarzoma sun kona akalla motoci dari uku da arbain da uku, kamar yanda yansanda suka sanar.

A birninNew York na Amurka ma duk da sanyin da ake da dusar kankara dake zuba dubun dubatar jama sun hallara a dandalin nan na Times suna kade kade da raye raye da wasan tartsatsin wuta domin murnar shigowar sabuwar shekarar.