1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Merkel za ta gana da shugabannin Afirka

Abdul-raheem Hassan
October 30, 2018

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel za ta karbi bakuncin wasu shugabannin kasashen Afirka domin gudanar da babban taron koli na karfafa gwiwar zuba jari a nahiyar.

https://p.dw.com/p/37MOz
Deutschland G20 Afrika Treffen
Hoto: Getty Images/AFP/J. Macdougall

Taron shi ne irinsa na farko da za a yi domin waiwayen shekara guda bayan kaddamar shirin bunkasa tattalin arziki da zuba jari a nahiyar Afirka da aka yi a shekarar 2017. Shugaban kasar Masar Abdel Fattah al-Sisi zai yi ganawa ta musamman da Merkel daura da taron, inda za su tattauna kan kulla dangantakar kasuwanci tsakanin Jamus da Masar.

Shugabannin kasashen Afirka 11 za su halarcin taron kolin, inda Shugaban gwamnatin Ostiriya Sebastian Kurz zai halarci taron. Yayin gudanar da taron kasashen masu ci gaban tattalin arziki wato G20 da aka yi bara a Jamus, Merkel ta kaddamar da shirin na musamman da zai habaka kasuwanci da tattalin arzikin nahiyar Afirka.